TARIHIN ASALIN ZAMFARAWA

 



Hon. Ibrahim Ɗan madamin Birnin Magaji


A Birnin dutsi wanda a halin yanzu yana karkashin masarautar zirmi dake jihar Zamfara, to a nan ne akace zamfarawa suka fara yada zangonsu, a lokacin da suka riski kasar Hausa daga wurin da suke zaune na Gabas ta tsakiya.


 Jagoran su, da ake kira Dakka ne ya fara Sarauta a wannan Gari na Dutci/Dutsi a wajajen Shekarar 1300 AD.

 Ance Waɗan nan Mutanen (Zamfarawan Farko ) masu tsayi ne da girman jiki  sosai , kusan wannan ne dalilin da ke sanyawa ana alaƙan ta su da Jinsin Samudawa. 

Haka kuma Kaburburan su da ke Dutci /Dutsi a halin yanzu ma wani babban misali ne na irin girman Jikin nasu. 

Bayan Mutuwar Sarki Dakka Wanda shine Mahaifin Sarauniya Argoje/Yargoje, an yi Sarakuna biyu kafin ta samu damar ɗarewa kan Karagar Mulki.

 Ance Ƴargoje tayi Mulki a tsakiyar ƙarni na 13 miladiyya. 

 Kuma ta Shahara a lokacin ta , domin har a dajin Kuyambana da ke ƙasar Ɗansadau ta Jahar Zamfara ta yanzu takan Zauna da Majalisar ta , tana yanke hukunci akan lamurran da suka shafi al'ummar ta.

A Yanzu haka akwai wata fitilar ta da ke ajiye a ginin hukumar Adana Kayan Tarihi da al'adun Gargajiya na Jahar Zamfara wanda ake dangantawa da ita.

 Bayan Rasuwar ta a Dutci /Dutsi sai aka naɗa ƙanenta mai suna Bakurukuru a matsayin Sabon Sarki. 

Sarki Bakurukuru ɗan Dakka ne ya ƙirƙiri Sabuwar Hedikwatar Zamfarawa,  Mai Suna Birnin Zamfara daga ƙarshe-ƙarshen ƙarni na 13 zuwa farko-farkon ƙarni na 14 , shune silar da zamfarawan suka tashi daga Dutci/Dutsi zuwa can Birnin Zamfaran, inda sunan Gonar Alkalin Zamfarawan ya amshe sunan Birnin na Zamfara. 

A Wannan Wuri ne suka yi Mulki har lokacin da Gobirawa suka ƙwache Birnin daga hannun su a cikin ƙarni na 17.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post