Mutane da dama sun kasa fahimtar kalmar Kimiya da Fasaha. To ita dai wannan kalma ba kalma daya bace, kalmo guda biyu ne suka hadu suka zama daya ko nace suka bada ma'ana daya.
Toh ilimin kimiyya da fasaha ilimi ne na zamani da ya kunshi bincike a fannukan ilimi daban daban, akan dukkan halittun da Allah ya yi doron kasa.
A yau muna cikin rayuwa ne wanda komai mun daura shi akan bincike, muna bincika mene ne wannan ko wancan abun?
Yaya yake kuma a wani mataki ake amfani dashi?
Idan mun tattara wannan bayani sai kuma mu watsa wannan bincike a duniya domin mutane su san gaskiyan binciken da aka yi. Mu a fannin mu na information technology Mun bada muhimmanci akan bayani, bayan an samu bayanin sai kuma mu san hanyar da za a yada wannan bayanin....
To duka-duka anan muka kawo karshen wannan shiri na mene ne Kimiya da Fasaha wannan ni Abubakar Saleh AlQuyraemey na gabatar sai kuma wani lokacin idan Allah mai komai ya sake sadamu, zaku iya ajiye mana comments a ƙasa domin tambayarmu abinda ya shige maku duhu.