Assalamu alaikum jama'a barkanku da wannan lokaci, bakanmu da kasancewa a cikin wannan site namu mai albarka, wato kimiya da fasaha tv. Shi dai wannan site zai dinga zakulo maku abubuwan kimiya da kuma fasahohi daban daban domin sanar da al'umma, da fatan zaku bamu goyon baya.
To a yau maudu'in mu zamuyi magana ne akan yadda zaka yi bayani ne akan waÉ—anda suka cike "N-POWER C" watanni goma da suka wuce.
Ana sanar da wadanda suka cike "N-POWER C"cewa gwamnatin shugaba Buhari ta fitar da website na musamman domin tan-tance sabbin ma'aikatan N-Power zango na uku, wato "N-POWER beneficiaries Verification".
Za'a shiga wannan site dinđŸ‘‡
Domin canza Password din su, dan shine hanya ta farko na Verification din.
Bayan an shiga za'a ga wurin da aka rubuta "Forgot password".
Wannan wurin za'a danna, idan ya hude zai nuna wurin da za'a sa email address. Bayan an sa, sai ayi sending, daga nan zasu tura sako zuwa email din ka.
Sai a shiga email din, a bi link din da suka tura na reset password ko Change password.
Bayan nan sai ka saka registration number dinka.
Shine lambar da aka baka lokacin da kayi applying N-POWER a 2020.
Za'a ga ya fara da (NA1234567) misali.
Daga nan za'a ga column gudu biyu, wato wasu wurare, sai a shiga na farko a saka registration number din.
Sai a shiga column na biyu a maimaita abinda aka saka a column na farko.
Daga nan zasu tura sako zuwa email idan anyi dai dai babu kuskure.
Daga nan kuma sai a koma wancan link din da na kawo na farko, watođŸ‘‡
aje ayi login, wato a shiga.
A wannan wurin Login din kuma ana bukatan email address dinka ne, da password din da ka canza, ko ka sanya.
Idan ya bude kuma za'a ga sauran bayanan da suke bukata.
Allah yasa a dace da alkhairi dake cikin wannan shiri.
Wanda yake da 'korafi, ko tambaya, sai ya tura musu da sako ta email address din su kamar haka:đŸ‘‡
npower@nasims.gov.ng
A daure ayi wannan verification din, saboda da zaran an kammala za'a sake sunayen wadanda suka yi nasarar shiga shirin na N-POWER, kar a manta Baba yace a dauki mutane miliyan 'daya ne, ba dubu dari biyar da aka saba ba.
Allah ya 'kara taimakon shugaban mu, shugaba Muhammadu Buhari.