Ta faru ta kare inji hausawa, a jiya ne babban daracta nan Malam Aminu Saira ya wallafa a shafin sa na Instagram cewa, nan da sati ɗaya zasu kammala daukar shirin ‘LABARINA SERIES’ wanda shahararren marubucin nan wato Malam Ibrahim Birniwa ya rubuta.
Babban daraktan ya ci gaba da cewa haƙiƙa bayan wuya sai daɗi, bayan kiraye-kirayen da jama'a suka rinƙa yi na cewar yaushe za'a dawo wannan kasaitaccen shiri, wanda ya ke haska wa al'umma Adabi su.
To daga karshe dai shima shirin ‘LABARINA SERIES’ zai bi tagwayen finafinai yan uwansa irin su: Kwana Casa'in da kuma Gidan badamasi, sai dai abin tambaya anan shine shin a wace tasha za'a dinga kallon shirin ‘LABARINA’ domin munji cewar an raba hannun riga tsakanin daraktan da kuma tashar Arewa 24 wadda ada ta kawo shirin.
Hakika wannan Kashi na Uku zai zo da abubuwan mamaki duba da a kashi na biyu an nuna cewar an kama presdor sai dai kuma kwatsam! Sai gashi an gano shi a kashi na uku yana ba Sumayya fulawa, tambaya anan ita ce shin sakinsa aka yi ko ko me ya faru? Amsar dai na a 'LABARINA' kashi na Uku da muke tsumayen fitowar sa.
Ga wasu hotuna nan comments da masoyan wannan shiri na Labarina suka yi daga ƙasa.