‘Yan bindiga sunyi awon gaba da mutane a Abuja sun bukaci miliyan 200 Kudin fansa

 



A ranar Larabar nan ne wasu 'yan bindiga suka sace wasu mutane 4 mazauna garin kiyi da ke garin kuje a babban birnin tarayya (FCT). Inda suka yi awon gaba da mutane hude (4). 

Jaridar Daily Trust ta ce, a cikin wadanda aka sace harda wani minista mai suna Salami Olalekan, wanda ya kasance memba ne a ma'aikatar Hukuntar Raya Babban Birnin Tarayya (FCTA).

Walliam Salami wanda ya kasance yaya ne a wajen Olalekan ya ce, masu garkuwar sun nemi Naira miliyan 200 a matsayin kuɗin fansa, Naira miliyan 50 ko wanne mutum daya.

Ya kuma ci gaba da cewa, "Masu garkuwar sun kiramu a waya suna bukatar miliyan 50 akan duk mutum daya.”

An gano cewa ragowar mutane ukun da aka sace sun hada da wani direban tasi, dan acaba da kuma dayan wanda har yanzu ba a tabbatar da gano shi ba.

Kakakin rundunar Yan sanda birnin tarayyar Abuja ASP Mariam Yusuf, ta tabbatar da sace mutanen, inda ta ce rundunar su na kan ƙoƙarin ta kwato mutanen daga hannun masu garkuwar.

To fatanmu anan shi ne Allah Ya shiga tsakanin na gari da mugu. Amin


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post