Sakamakon gazawar yan kasa na bin dokokin da gwamnatin Najeriya ta gindaya akan rijistar NIN, gwamnatin ta yanke shawarar kara wa'adin ne ayau din nan. Hakika wannan labari zai zama mai daɗin gaske ga 'yan ƙasa wadanda basu samu damar yin katin dan kasa ba.
19 ga watan Janairu ita farkon ranar ƙarshe amma, an koma zuwa 9 ga Fabrairu, daga baya kuma aka maida ta zuwa 6 ga watan Afrilu, yanzu 6 ga Mayu kenan an kara wata 1. Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, "Rashin saka lambobin NIN na nuna cewar mutum ya yi rashin biyayya ga dokoki da ka'idojin da ke a cikin tsarin kundin mulkin kasa, kuma zai iya haifar da daurin zaman gidan yari. Don haka, ana shawartar 'yan ƙasa da su yi amfani da wannan lokacin da su ke da shi don yin rijistar NIN ɗinsu don guje wa hukuncin da ke tattare da hakan.
Wasu daga cikin abubuwan da mutum zai fuskanta idan har ya gaza saka NIN dinsa a cikin layin wayarsa shine; Mutum zai rasa layinsa dungurugum, ba zai iya yin kira ko karɓar kira tare da wannan layin ba kuma an katange shi kai tsaye daga cikin layukan sadarwa daga cibiyar bayanai ma'ana anyi block dinsa har a bada, kuma bazai taɓa buɗuwa ba). Idan hakan ta faru, dole ne wannan mutumin ya sayi sabon layi wanda ba abu ne mai sauƙi ba a wannan, domin farashin sa na siye da rajistar layin zai kai kusan naira dubu bakwai (₦7000).
Don haka, yana da kyau mutane suyi amfani da wannan dama, Idan bakayi rijistar NIN ɗinka ba ko kuma haɗa shi da layin wayarka ba, sai ka yi kafin ranar 6 ga watan Mayu.
